Skip to main content

Posts

RINJAYYAR SHA'AWA A SOYAYYA

RINJAYAR SHA'AWA A SOYAYYA Ayeesh A. Sadeeq LubnaSufyan Email: matsalarmaaurataayau@gmail.com Text or whatsapp : 09066027420                                  09028787443 Blog: matsalarmaaurataayau.blog.spot.com Muna cikin wani zamani da sai dai muce Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun! Ina tunaninmu? Ina hankalinmu? Ina ilimin addininmu? Ina al'ada da kunyarmu? Ina kyawawan dabi'unmu? Kaicona! Mun yi watsi dasu, mun ari al'adu da dabi'un masu jajayen kunnuwa mun yafa ma kawunanmu. Haba matasa! Kune fa iyayen gobe, shin idan ba ku gyara munanan halayenku ba kuna tunanin yayanku zasu yi? Mun dau tura hotunan tsiraici da kalaman batsa a matsayin soyayya, mun rushe tubalin soyayya da kauna yar usuli. Mun dau hakan a matsayin wayewa. Wannan wace irin lalatacciyar wayewa ce mara tushe da asali? Shin ba ma yi ma kanmu ka...
Recent posts

KOMAI YA CANZA

KOMAI YA CANZA LubnaSufyan Email: Calmlubna@gmail.com matsalarmaaurataayau@gmail.com Kafun muyi aure akwai fahimta a tsakanin mu. Kalmar 'Kayi hakuri' ko 'Kiyi hakuri' bata mana nauyi. Saurin yafewa juna baya bamu wahala. Hankalin mu baya kwanciya in bamuji muryar junan mu ba. Kulawar nan mai wuyar mantawa. Kira da bukatar jin dayan mu yaci abinci, nutsuwa kanyi karanci ga dayanmu inhar dayan bashi da lafiya. Kyautuka lokaci zuwa lokaci. Dukkan tunanin mu ya ta'allaqa kan cewar da zarar munyi aure, shaquwar dake tsakanin mu kafun auren, kulawa da dukkan fahimtar nan zasu karu, to meye ma zai hana hakan faruwa? Bayan bamuda burin da ya wuce mallakar juna. KOMAI YA CANZA daga bangaren ka, bansan me yasa ba, bansan ko samuna da kayi bane yasa kake ganin yanzun bana bukatar kulawar ka. "Ina sonki..." Dana kanji fiye da goma a rana kafun auren mu, yanzun ko daya banaji bayan auren mu. Me yasa zaka sabamun da abinda kasan bazai dore ba? Me yasa zaka da...