RINJAYAR SHA'AWA A SOYAYYA Ayeesh A. Sadeeq LubnaSufyan Email: matsalarmaaurataayau@gmail.com Text or whatsapp : 09066027420 09028787443 Blog: matsalarmaaurataayau.blog.spot.com Muna cikin wani zamani da sai dai muce Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun! Ina tunaninmu? Ina hankalinmu? Ina ilimin addininmu? Ina al'ada da kunyarmu? Ina kyawawan dabi'unmu? Kaicona! Mun yi watsi dasu, mun ari al'adu da dabi'un masu jajayen kunnuwa mun yafa ma kawunanmu. Haba matasa! Kune fa iyayen gobe, shin idan ba ku gyara munanan halayenku ba kuna tunanin yayanku zasu yi? Mun dau tura hotunan tsiraici da kalaman batsa a matsayin soyayya, mun rushe tubalin soyayya da kauna yar usuli. Mun dau hakan a matsayin wayewa. Wannan wace irin lalatacciyar wayewa ce mara tushe da asali? Shin ba ma yi ma kanmu ka...