Skip to main content

KOMAI YA CANZA

KOMAI YA CANZA

LubnaSufyan

Email: Calmlubna@gmail.com
matsalarmaaurataayau@gmail.com

Kafun muyi aure akwai fahimta a tsakanin mu. Kalmar 'Kayi hakuri' ko 'Kiyi hakuri' bata mana nauyi. Saurin yafewa juna baya bamu wahala. Hankalin mu baya kwanciya in bamuji muryar junan mu ba.

Kulawar nan mai wuyar mantawa. Kira da bukatar jin dayan mu yaci abinci, nutsuwa kanyi karanci ga dayanmu inhar dayan bashi da lafiya. Kyautuka lokaci zuwa lokaci.

Dukkan tunanin mu ya ta'allaqa kan cewar da zarar munyi aure, shaquwar dake tsakanin mu kafun auren, kulawa da dukkan fahimtar nan zasu karu, to meye ma zai hana hakan faruwa? Bayan bamuda burin da ya wuce mallakar juna.

KOMAI YA CANZA daga bangaren ka, bansan me yasa ba, bansan ko samuna da kayi bane yasa kake ganin yanzun bana bukatar kulawar ka.

"Ina sonki..."

Dana kanji fiye da goma a rana kafun auren mu, yanzun ko daya banaji bayan auren mu. Me yasa zaka sabamun da abinda kasan bazai dore ba? Me yasa zaka daga burin zuciyata har haka? Kafin auren mu ko hoto na ka gani sai ka yaba. Yanzun gani a gidanka, tunda safe nayi wanka nayi kwalliya.

"Kinyi kyau"

Kalma biyu inka fadamun zuciyata zatai sanyi. Na wuce ta gabanka yafi sau goma, yanayin ka bai nuna kaga kwalliyar da nayi ba. Bayan wannan, dukkan kulawar gidanka tana karkashina yanzun, abincinka, yaran mu, duk wasu aikace aikace da bukatunka. A cikin wata sau daya, ban bukata da yawa ba. Sau daya inka kalleni kace

"Allah ya saka miki da alkhairi da dukkan kokarin ki akan mu"

Shi kadai ya wadatar, basaika fadamun kullum ba. Lokaci zuwa lokaci ka yaba kokari kamar yanda kakeyi kamun auren mu idan na ware lokaci ko text nai maka.

KOMAI YA CANZA. Kamun auren mu duk wasu kananan halayena marassa kyau kana kauda kai a kansu, ko da na maka laifi na dawo na baka hakuri kaine kake fadamun cewar kasan ni mutum ce, dole akwai abinda bazai cika a tare dani ba. Kana mun uzuri a lokutta da dama, ba ko da yaushe kake daga muryarka akaina ba.

Amman yanzun abu kadan, laifin da kamun auren mu in na maka shi murmushi zakai ka share, shine kake gaba dani akai na tsayin kwanaki. Na baka hakuri akanshi yafi a kirga amman kamar ina tunzura ka ne.

KOMAI YA CANZA, kai da kanka ka canza mun, zuciyata takanji kamar ba nawan bane kai, nakan tuna dukkan alkawurran ka akaina, nakan ji daman bakai mun su ba, kilan da canzawar da komai yayi bai dameni har haka ba.

KOMAI YA CANZA. Da duk wani lokacin ka tare dani kake yinshi. Amman yanzun fita yawo da abokan ka yafi ye maka zama kaji matsalata. Me yasa ka dauka dan na aureka banda sauran damuwa da nake bukatar kaji? Ka sha fadamun ni kadai na isheka rayuwa, badan na yarda da hakan ba, badan ban taba tunanin zakai sha'awar kara aure ba. Amman watan mu nawa? Harka fara kula wasu a waje. Me ya canza?

Dan Allah ko bamu koma kamar da ba mu kamanta, ka koyi yafe mun da wuri kamar da, kamun auren mu ma ina maka laifi balle yanzun da zaman har abada ya kama mu. Ka kalleni sosai, ka kalli cikin idanuwa na. Ni ce fa, ina soyayyar da kake mun? Burin ka aure na fa, ka samu yanzun, me yasa kake wasa da hakan?

KOMAI YA CANZA. Kamun auren mu dake, a rana kina mun text yafi goma, wani lokacin dan kiji ya kasuwa ko ya wajen aikina, wani lokacin dan kawai kina kewata ne. Ko ban reply ba suna mun dadi. Suna sa inji dan nisan da mukai da juna baisa nabar tunanin ki ba.

Yanzun da mukai aure rabon da ki bani wannan kulawar harna manta, mun kwana waje daya, mun tashi tare, nasan in na dawo kasuwa ko office zan sameki, amman waya fada miki dan na zama mallakin ki yanzun bana bukatar kulawar nan? Wayace miki bazanji dadi ba inkin turamun text din da kika saba ko da baikai yawan wancan ba.

KOMAI YA CANZA. Kinsan ni namiji ne mai son kwalliya, na sha fada miki, hakan yasa kike kasancewa cikin kwalliya duk sanda zanzo wajen ki. Me yasa yanzun inba unguwa zaki je ba bakya mun? Nace miki na daina so ne? Nakan daure zuciyata da kama hannun ki saboda kunshin da suke kasancewa a jikin su. Yanzun zan iya yin hakan, na nemi kunshin na rasa. Me yasa?

Kamun muyi aure, har kishin ki kike nunawa in nayi kwalliya ko shiga me kyau saboda kyan da nayi bakya so wasu matan su kalla. Amman yanzun duk yabon nan bana samu balle ma inyi tunanin kin damu. Waya ce miki dan munyi aure na daina bukatar jin har yanzun ina da kyau a idanuwanki.

KOMAI YA CANZA. Kafun muyi aure kina kaffa-kaffa da bacin raina, sosai kike kauce ma duk wani abu da kikasan zai bata mun rai, amman yanzun kikan sa inji kaman wani lokacin da gangan kikeyin wasu abubuwan dan kinsan raina zai baci. Kafun muyi aure in kika batamun rai kina bani hakuri, amman yanzun hakan na miki wahala, me yasa?

KOMAI YA CANZA. Kafun auren mu muryarki kasa take da tawa a koda yaushe, baki taba daga mun murya ba, akwai wannan respect din a tsakanin mu, ko da kina da abin fada kikan saurara sai na gama magana sannan kimun bayani a nutse. Amman yanzun lokutta da dama har makota kan jiyo harshenki akaina, bakya tauna duk wata magana kamun ki furtamun ita. Ina dukkan mutuntawar nan ta tafi? Ina kwarjinin da nake dashi a idanuwanki?

Da bakya rasa labarin da zaki bani, bama rasa abinda zamu fada a tsakanin mu. Hakan yasa duk wani lokacina nake son yinshi tare dake. Amman yanzun zamu iya zaman awa daya batare da abin fada ba. Babu kwalliyar nan, babu nuna mun kaunar nan. Saboda me zan zauna a gida? Saboda me bazan fita yawo da abokaina ba? Saboda me bazan fara tunanin kara wani auren ba? Bayan kin kasa bani dalilin kin yin hakan?

BAN GAMA BA. ZANCI GABA IN SHAA ALLAH. BARI INJI RA'AYOYINKU AKAN WANNAN. ALLAH YA DATAR DAMU. AMIN THUMMA AMIN.

Comments

  1. This is very interesting. May we continue to maintain the standard we set in our courtship.

    ReplyDelete
  2. Interesting. Allah ya bamu mata na gari kuma ya bamu ikon sauke hakkokin matan mu,amin.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

RINJAYYAR SHA'AWA A SOYAYYA

RINJAYAR SHA'AWA A SOYAYYA Ayeesh A. Sadeeq LubnaSufyan Email: matsalarmaaurataayau@gmail.com Text or whatsapp : 09066027420                                  09028787443 Blog: matsalarmaaurataayau.blog.spot.com Muna cikin wani zamani da sai dai muce Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun! Ina tunaninmu? Ina hankalinmu? Ina ilimin addininmu? Ina al'ada da kunyarmu? Ina kyawawan dabi'unmu? Kaicona! Mun yi watsi dasu, mun ari al'adu da dabi'un masu jajayen kunnuwa mun yafa ma kawunanmu. Haba matasa! Kune fa iyayen gobe, shin idan ba ku gyara munanan halayenku ba kuna tunanin yayanku zasu yi? Mun dau tura hotunan tsiraici da kalaman batsa a matsayin soyayya, mun rushe tubalin soyayya da kauna yar usuli. Mun dau hakan a matsayin wayewa. Wannan wace irin lalatacciyar wayewa ce mara tushe da asali? Shin ba ma yi ma kanmu ka...