RINJAYAR SHA'AWA A SOYAYYA
Ayeesh A. Sadeeq
LubnaSufyan
Email: matsalarmaaurataayau@gmail.com
Text or whatsapp : 09066027420
09028787443
Blog: matsalarmaaurataayau.blog.spot.com
Muna cikin wani zamani da sai dai muce Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun!
Ina tunaninmu?
Ina hankalinmu?
Ina ilimin addininmu?
Ina al'ada da kunyarmu?
Ina kyawawan dabi'unmu?
Kaicona!
Mun yi watsi dasu, mun ari al'adu da dabi'un masu jajayen kunnuwa mun yafa ma kawunanmu.
Haba matasa! Kune fa iyayen gobe, shin idan ba ku gyara munanan halayenku ba kuna tunanin yayanku zasu yi?
Mun dau tura hotunan tsiraici da kalaman batsa a matsayin soyayya, mun rushe tubalin soyayya da kauna yar usuli. Mun dau hakan a matsayin wayewa. Wannan wace irin lalatacciyar wayewa ce mara tushe da asali? Shin ba ma yi ma kanmu karatun ta natsu ba?
A matsayinki na mace da kunya aka sanki, amma yanzu ta kai ta kawo mata an binne wannan kunyar. Namijin da ba mijin aurenki ba, kin dau duk wasu bukatu na shi kin aza bisa kanki. Idan sha'awar shi ta taso kece mai kauda ma sa wannan sha'awar, ta hanyar maganganun batsa da tura masa hotunan sassan jikinki.
Haba yaruwa! Kin taba tunanin koda na sakan guda ne, idan ba ki aure shi ba, idan Allah ya karbi ranki a wannan lokacin fa? Kamun muzo nan, idan wani sabani ya shiga tsakanin ku ya baza hotunanki a duniya ya zakiyi?
Kun dauki son zuciya, sai an samu matsala kuce zaku labe a bayan shaidan ko? Ko ku dauki girman laifinku ku dora kaco kan akan Kaddara. Yar uwa na matsa maganata akan ki ne saboda ke macece, akwai dalilai da dama da yasa Allah ya daga darajarki!!!
Kinsan idan hoton nan ya fita kin gama yawo ko? Ke bama ke kadai kika gama yawo ba, harda daraja da martabar iyayenki. Suna iya kokarin su, sannan kinsan sai wani ikon Allah ke da samun miji nagari ko? Wallahi ki tuba kamun lokaci ya kure miki.
Ko kinsan da wahala ya aureki? Kina mamaki ko? Dan iska ne shi ko mahaukaci da zaku gama watsewar yace zai aureki? Komin lalacewar shi fa yana son kimtsatsiya. Ko ya aureki ba wata daraja zakiyi a idanuwan shi ba. Babu abinda bai rigada yagani ba. Me zaki kai mishi kuma? Wata daraja duk baki da ita a idanuwan shi.
Ke kenan cikin tashin hankali. Dakin ganshi da waya yana danne-danne zaki dauka fa abinda kukayi ne yakeyi da wasu yan matan. Me akace kiyi a irin yanayi na sha'awa?
Kai ma harda kai, aturunga, kurungu muqarabban shaidan, ka samu yar mutane kana dorata a hanya kuna lalacewa, sannan ku gama kace kai saita gari ko? Kasan ba tukunyar kasa bace balle ka kwankwasa kaji ko? Yanda babu wanda yasan abinda ya faru tsakaninka da waccen sai Allah, haka wadda duk ka kwaso a matsayin ta gari zata kasance.
Kun samu sabani, hanya daya kake da ita da zaka rama, ka yada hotunan ta da ta aiko maka. Ku dukanku sabo kuke aikatawa, ku dukan ku daudar zina na tattare daku inhar baku tuba ba. Amman ka tsaya na minti daya kai tunani mana, kasan girman abinda ka akaita mata kuwa? Duk da ta wanni fannin banga laifinka ba. Koba komai ita ta fara shirmen yarda da kai da dora farin cikin ka akan addininta.
Babu fa biyayya ma abokin halitta wajen sabawa umarnin Ubangiji. Kina tunanin idan baki yi abinda yace ba shikenan zai tafi ya bar ki, ba zai aure ki. Wai to shi kadai ne autan maza? Idan ya qi maza dubu zasu so ki, dama can ba mijinki bane ba, ke ba ki ma cancanci zama da fasiqi irinsa ba. Tun wuri kiyi ma kanki karatun ta natsu, kisan cewa ita fa mace rayuwarta a waje kayyadadda ce, sannan fadi gareta.
Ya za ki ji a ranar da kika hadu da abokin watsewarki a matsayin kanin mijinki, yayan mijinki, abokin mijinki, cousin din mijinki? Kina tunanin akwai sauran mutunci a tsakanin ku? Wallahi Allah babu, kadan daga ciki ne zasu rufa ma ki asiri, wasu kuwa kamar dama jira suke su samu wannan opportunity din, kafin aje koina aurenki ya mutu, kin ji dadi kenan? Babu dadi ko kadan a wajen sabon Allah, ki tuba kafin Allah ya karbi rayuwarki.
Namiji a duk inda kake kai shugaba ne, kuma a kaifin tunani ka dara mace, idan ba zalunci ba ka samu yarinya da ke matukar sonka, sai kayi amfani da wannan son wajen wargaza farincikinta, saboda kasan ba zata iya musanta ma ka ba. Mace na da rauni a soyayya, domin itace abu mafi saurin dagula lissafin ya mace.
Idan ka lalata diyar wani kana ganin kasha lallai wallahi Allah sai ya bi ma ta hakkin zaluncin da kayi ma ta, alkawari ne kaima sai anyi ma na jininka wanda za ka fi jin zafi. Ina amfanin irin rayuwar?. Allah ya datar damu. Amin thumma amin
Ameen ya Allah.
ReplyDeleteAllah ya sa mu gane baki daya.
Ameen amin. Allah yasa mu dace kuma yasa mu gama lafiya.
ReplyDelete